140126murtala.m4a
|
Kungiyar wasan kwallon kafar kasar Najeriya, Super Eagles, ta samu nasarar tsallakewa zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin kasashen Afirka ta 'yan wasan gida da ake gudanarwa a halin yanzu a kasar Afirka ta Kudu.
Najeriya ta samu nasarar ne bayan da ta doke kasar Morocco da ci hudu da uku a yammacin ranar jiya Asabar.
Kungiyar Morocco ce ta fara zura kwallaye uku a ragar Najeriya kafin daga baya Najeriya ta farke ta zura kwallaye uku gami da kara kwallo guda da ta ba ta damar tsallakewa.
Dan wasan Morocco, Moutaouali ne ya fara zura kwallo a mintuna na 33, Mouhssine ya zura ta biyu a mintuna na 37, yayin da Moutaouali ya sake zura ta uku a mintuna na 40.
Jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Uzochukwu ya zurawa Najeriya kwallo ta farko a mintuna na 49, sai Rabi'u Ali a mintuna na 55 ya kara ta biyu, Uzoenyi ne ya farke kwallo ta uku a mintuna na 90, sai kuma Ibrahim ya zura kwallon da ta baiwa Najeriya nasara a mintuna na 111 bisa karin lokaci. (Murtala)