in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire na bisa hanya mai kyau ta bunkasa tattalin arzikinta, in ji IMF
2013-08-09 10:39:46 cri

Wakilin asusun ba da lamuni na duniya IMF dake zaune a kasar Cote d'Ivoire Wayne Kamar ya bayyana a ranar Alhamis a birnin Abidjan cewa, kasar Cote d'Ivoire tana bisa hanya mai kyau ta fuskar bunkasa tattalin arziki.

'Kasar Cote d'Ivoire na bisa hanya mai kyau ta fuskar bunkasa tattalin arzikinta a cikin wannan shekarar 2013 kamar yadda alkaluma suka nuna.' in ji mista Kamar a yayin wata hirarsa tare da 'yan jarida. Jami'in ya nuna yabo kan yadda ayyukan sarrafawa suka karu a kasar Cote d'Ivoire, bisa jawadalin aikin shugaban kasar na baiwa wannan kasa damar kasancewa cikin kasashe masu samun cigaban masana'antu da tattalin arziki zuwa shekarar 2020.

A wannan shekara, alkaluma zuwa cikin rabin shekara sun fi kyau.' in ji mista Wayne Kamar, lamarin dake shaida cewa, kasar tana fatan cimma burin samun bunkasuwa da ta tsaida.

Asusun IMF ya amince wa kasar Cote d'Ivoire da wani tsarin tattalin arziki na shekaru uku masu zuwa na kimanin dalar Amurka miliyan 616.

Kuma a yawancin wasu lokuta, kwararrun wannan hukuma sun yi hasashen samun bunkasuwa mai karfi a cikin wannan kasa da za ta janyo moriya ga mutanen kasar Cote d'Ivoire.

Gwamnatin kasar Cote d'Ivoire ta bayyana cewa, a cikin wannan shekarar 2013, za a cimma kashi 9 cikin 100 na bunkasuwa wadda za a ga kashi 10 cikin 100 zuwa shekarar 2014. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China