Djotodia ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da shugaban kasar Congo Denis Sassou Nguesso, a garin Oyo dake arewacin kasar ta Congo. Har ila yau shugaban ya ce kafa sabuwar gwamnati na cikin manyan ayyukan da aka dorawa firaministan wucin gadin kasar Nicolas Tiangaye nauyin aiwatarwa. Ban da batun kafa sabuwar gwamnatin, shugaba Djotodia ya ce akwai shirin jibge rundunonin soji a dukkanin lardunan kasar, tare da batun kwance damarar yaki, musamman a helkwatar kasar dake birnin Bangui, matakin da ake sa ran kammalawa nan da makwannin biyu ko uku masu zuwa. (Saminu Hassan)