140105murtala
|
Gwamnatin jihar Yobe dake arewa maso gabashin tarayyar Najeriya ta ware zunzurutun kudi na sama da Naira biliyan dari a matsyain kasafin kudin wannan sabuwar shekara ta 2014.
Da ya ke gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokokin jihar a babban dakin taron muhawara na majalisar dake birnin Damaturu, gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Geidam ya ce wannan kasafin kudi na bana, kasafi ne da aka masa lakabin kasafin kudi na samar da abubuwan more rayuwar al'umma da kuma inganta tattalin arzikin jihar.
Ya kara da cewar a kasafin kudi na wannan shekara, gwamnati na da kudurin gudanar da ayyuka masu matukar muhimmanci, tare da kammala sauran ayyukan da aka fara da kuma aiwatar da ayyuka sababbi da suka hada da gina sababbin hanyoyin mota a kowane bangaren jihar, da samar da ilmi mai inganci da harkokin kiwon lafiya da sauransu.
Ma'aikatun da suka fi samun kaso mai tsoka sun hada da ma'aikatar kwadago , sai kuma ma'aikatar ilmi da ta zo ta biyu.
Haka kuma gwamna Alhaji Ibrahim Geidam ya nemi al'umma da su kokarta wajen bada hadin-kai ga hukumomin jihar ta yadda zasu samu damar aiwatar da dukkan manufofinsu na ciyar da jihar gaba, da kuma ci gaba da samar da zaman lafiya mai dorewa.
Da yake bayani a yayin karbar wannan kasafin kudi, kakakin majalisar dokokin jihar Yobe Alhaji Adamu Dala Dogo ya bada tabbacin cewa majalisar zata duba wannan kasafin kudi cikin kankanin lokaci domin bada amincewarta bisa zummar ganin al'ummar jihar ta ci gajiyarsa.(Murtala)