140114murtala
|
Shugaban tarayyar Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya sanya hannu kan dokar haramta auren jinsi guda da duk wata mu'amula da ta shafi luwadi da madigo kamar yadda kakakinsa Reuben Abati ya bayyana jiya.
Reuben Abati ya ce tun a farkon wannan wata, shugaban ya sanya hannu don amincewa da dokar, sai dai bai bayyana ranar ba.
"Sama da kashi 90 cikin 100 na al'ummar Najeriya suna kalubalentar auren jinsi guda, saboda haka dokar ta dace da tsarin al'adunmu da kuma addinanmu", in ji Abati.
Sa'annan ya ce, bisa dokar Nijeriya, daga yanzu an haramta duk wata kungiya ta luwadi, madigo da makamantansu, don haka idan aka kama masu yin haka, za'a yanke musu hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.