A ranar Alhamis ne a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, gwamnatocin Najeriya da Burtaniya suka sanya hannu kan yarjejeniyar musayar fursunoni wato (PTA), ta yadda za a maido da 'yan Najeriya 521 da a halin yanzu suke zamansu na kaso a Burtaniya, kuma za su dawo gida su karasa wannan wa'adi.
Ministan shari'a na Najeriya mai shari'a Mohammed Adoke da takwartansa na kasar Burtaniya Jermey Wright ne suka sanya hannun a madadin kasashensu. Bisa sabuwar yarjejeniyar, ba za a bukaci amincewar fursuna ba kafin a maido da shi kasarsa ta asali, duk da cewa, gwamnatin Burtaniya ta yi alkawarin samar da Fam miliyan daya, ta yadda za a inganta yanayin gidajen yarin kasar ta Najeriya.
A jawabinsa, ministan shari'a na Najeriya, Adoke ya ce, sanya hannun kan wannan yarjejeniya, wata alama ce da ke nuna kyakkyawar dangantakar da ke wanzuwa tsakanin kasashen biyu, da kudurinsu na yin musayar fursunonin, matakin da ya ce, abin a yaba ne.
Ya kuma bayyana kudurin gwamnatin kasar ta Najeriya, na inganta rayuwar 'yan Najeriya da ke zaune a kasar ta Burtaniya.
Shi ma a nasa jawabin, ministan shari'a na kasar Burtaniya, Mr. Jermey ya ce, yana fatan a karshen wannan shekara, kasashen biyu za su nuna muhimmancin wannan yarjejeniya ta hanyar musayar fursunonin, da zarar ta fara aiki.
Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, ba dukkan 'yan Najeriya 521 da ke tsare a gidajen yarin Burtaniya ba ne za su amfana da wannan yarjejeniya, inda ya ce, wajibi ne wa'adin da aka yanke musu ya zarce watanni 12 kafin su ci gajiyar shirin. (Ibrahim)