in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 16 suka mutu a harin da aka kai a wani kauyen Najeriya
2014-01-08 14:13:57 cri

Hukumar 'yan sandan jihar Plateau dake tsakiya maso arewacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 16 a wani harin da aka kai a kauyen Shonong. Gawawwaki tara aka gano a wurin da aka kai harin na ranar Litinin yayin wasu gawawwaki bakwai aka kasa gane su sakamakon yadda suka kone, in ji kwamishinan 'yan sandar jihar Chris Olakpe a gaban 'yan jarida a birnin Jos, hedkwatar jihar. Akalla gidaje 20 aka kone, kuma ana cigaba da kokarin tantance adadin yawan mutanen da suka jikkata.

Mista Olakpe ya ce, ba a gano wadanda suka kai harin ba, amma ya tabbatar da cewa, 'yan sanda na cigaba da bincike har zuwa jihar Kaduna domin ganin an cafke wadannan 'yan bindiga.

Kwamishinan ya nuna cewa, hukumomin jihar na cigaba da tuntubar cibiyar 'yan sandan jihar Kaduna kan wannan lamari.

Mista Olakpe ya nuna cewa, jami'an tsaro na kokarin bullo da wasu sabbin dabarun magance hare-haren 'yan bindiga a jihar Plateau, tare da yin kira ga al'ummomin wurin da su ba da hadin gwiwa ga jami'an tsaro ta hanyar samar da bayanai ko shaidun da za su taimaka wajen gano mutanen da suka kai hare-hare kan al'ummominsu.

Wata majiyar 'yan sanda ta labarta wa manema labarai cewa, wasu 'yan bindiga sun kai hari a kauyen Shonong da misalin karfe bakwai na safe bisa agogon wuri a ranar Litinin tare da kashe mutane akalla 30. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China