Mr. Ban na daya daga cikin rukunin farko na manyan jami'an kasa da kasa da suka isa kasar Afirka ta Kudu, domin halartar bukukuwan jana'izar da gwamnatin Afirka ta Kudu ta shriya. Yayin ganawarsa da wakilan kafofin watsa labarai, Mr. Ban ya ce alal hakika rashin Mandela wani abun takaici ne ga daukacin duniya. Ya ce Nelson Mandela mutum ne da ya ba da gaskiya ga ayyukan tabbatar da adalci tsakanin 'yan dan Adam, da kuma kare hakkin dan Adam.
Har yanzu dai jama'ar kasar Afirka ta Kudu, da al'ummunomin kasa da kasa, su na ci gaba da nuna jimami da bakin ciki don gane da rashin wannan jarumi.
Yayin da Mr. Ban Ki-moon ke tunawa da ganawarsa tare da Mandela a shekarar 2009, ya bayyana cewa, halayyar tawaliwu ta tsohon shugaban ta burge shi kwarai, har ya zuwa yanzu kuma yana koyi da shi.
A Ranar 9 ga wata da yamma ne dai Mr. Ban da wasu jami'an MDD suka ziyarci asusun Nelson Mandela, da kuma wasu abubuwan tarihi dake bayyana zaman rayuwar Nelson Mandela. (Maryam)