131231-murtala
|
Gwamnan jihar Katsina dake arewacin tarayyar Najeriya, Alhaji Ibrahim Shema, ya bayyana cewa jihar za ta gudanar da zabukan kananan hukumomi da na kansilolinsu a wata na uku na na sabuwar shekara wato 2014.
Shema wanda ya bayyana hakan a yayin taron jam'iyyar PDP na yanki a jihar, ya ce za'a sanar da ranar yin zabe a watan Janairu, domin jam'iyyu su fara shiryen-shiryen shiga zaben.
Gwamna wanda Sanata Umar Tsauri ya wakilta, ya ce dukkan kayan aikin da za'a bukata yayin zaben an samar da su.
Tun lokacin da wa'adin shugabannin kananan hukumomin jihar 34 da kansulolinsu ya kare a farkon 2011, aka nada shugabannin rikon-gwarya har zuwa wannan lokaci.
"Za a gudanar da zaben a farkon sabuwar shekara, idan Allah ya yarda, saboda dukkan wani shiri da ya kamata an kammala shi", in ji Gwamna Shema.
Bugu da kari kuma, gwamnan yayi kira ga magoya bayan jam'iyyar PDP a jihar Katsina da su fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar zaben don zabar 'yan takarar da jam'iyyar za ta tsayar.
Murtala, wakilin sashin Hausa na CRI, daga Abuja, Najeriya.