A wannan rana da safe, hukumar FBI ta shirya wani taron manema labaru, inda wani jami'in ofishin hukumar FBI a yankin San Francisco David Johnson ya ce, wanda ya yi sarandan, sunansa Feng Yan mai shekaru 39, kuma ya daukin alhakin kunna wutar, ba ya da alaka da kungiyar ta'addanci, da siyasa, da hakkin bil adama. Feng Yan bai taba aikata laifi a baya ba, shi dan Amurka ne.
Za a kai kara ga Feng Yan bisa zargin sanya wuta da janyo barna ga kayayyaki, da kunna wuta ga karamin ofishin Sin a yankin San Francisco.
Amma, David Johnson ya ki fayyace hujjar aikata laifinsa ba.
Karamin ofishin jakadancin Sin a San Francisco ya ba da wata sanarwa, inda ya yi nuni da cewa, Sin ta yi la'akari da kokarin da Amurka ta yi game da lamarin, ta bukaci Amurka da ta gurfana da masu laifi a gaban kuliya. Kasar Sin za ta ci gaba da lura da abin da zai biyo baya game da lamari, kuma ta bukaci Amurka da ta dauki hakikanin matakai, don ba da tabbaci ga tsaro da mutunci na jami'an diplomasiyyan Sin a Amurka, don magance sake aukuwar irin lamarin. (Bako)