in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IDA ta baiwa Nijar tallafin kudi fiye miliyan 32 daga cikin gidauniyar DTS domin tafiyar da sauye-sauyen manufar bunkasuwa
2011-09-21 12:13:39 cri

Gwamnatin kasar Nijar ta sa hannu kan wani kuduri a ranar Talata da ta gabata dake ba ta damar amincewa kan yarjejeniyar karbar bashi tsakanin kasar da kungiyar ci gaban kasa da kasa wato IDA, bisa tushen gudanar da sauye-sauyen da suka shafi manufofin bunkasuwa da aka rattaba hannu a ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata.

Bisa yarjejeniyar bashin, kungiyar IDA dake cikin rukunin Bankin Duniya ta amince da bai wa kasar Nijar wani bashin kudi na darajar gidauniyar DTS miliyan 32.1 wato fiye da dalar Amurka miliyan 20.

Tallafin ya samu ne ta la'akari da wasu matakan da gwamnatin kasar ta dauka da suka shafi karfafa shiga takarar tattalin arziki ta hanyar rage kudaden takardu bisa kafa sabbin kamfanoni kan rajistan kasuwanci, rage kason haraji bisa cinikin kamfanoni da kuma sa hannu kan wani kundin haraji.

Haka wannan yarjejeniya ta shafi noma da ci gaban karkara, tare da sake manufar cibiyar samar da takin zamani da kayayyakin noma wato CAIMA da amincewar tsarin ayyukan fadakarwa na ci gaban aikin noma.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China