Nigeriya tayi alkawarin bada cikakken tsaro ga mahalarta taro na 30 na cibiyar D8 da za'ayi tsakanin 11 zuwa 14 ga watan Yuli a babban birnin Tarayyan Kasan, Abuja.
Babban magatakardar ofishin hulda da kasashen waje Martin Uhomoibhi ya bada wannan tabbacin a ganawar da yayi da jakadu da manyan kwamishinoni na mambobin kasashen D8 littinin din daya gabata kafin babban taron.
"Saboda tsaron lafiyan bakin mu muna son mu tabbatar cewa Ministoci,Kwamishinoni,Babban Magatakarda da sauran mahalarta taron zasu samu cikakken tsaro daga Gwamnatin Tarayyan Nigeriya"a cewar sa.
Yayi bayanin cewa an kammala dukkan shirye shiryen daya kamata don isowar Mahalarta taron.
Taron na 30 na cibiyar D8 zai yi nazarin matsayin aiwatar da shawarwarin da akayi a baya a muhimman wurare kamar kasuwanci,aikin noma da samar da abinci,hada kan masana'antu da kuma manya da kananan masana'antu har ma da sufuri. (Fatimah Jibril)