Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit ya bayyana a ranar Laraba da kafa dokar ta bace a jihohin Unites da Jonglei, in ji gwamnatin Sudan ta Kudu bisa shafinta na Twitter.
Dakarun 'yan tawaye dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar na rike da Bantio, hedkwatar jihar Unites mai arzikin man fetur.
Wani labarin ya ce, rundunar sojojin Sudan ta Kudu ta amince da cewa, 'yan tawayen sun karbe muhimmin garin Bor, hedkwatar jihar Jonglei a ranar Laraba, bayan da sojojin gwamnatin kasar suka fice daga birnin.
Domin kawo karshen tashe-tashen hankali a kasar Sudan ta Kudu, ana kyautata zaton cewa, birnin Addis-Abeba na kasar Habasha zai karbi wani zaman taron shawarwari tawagogin gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye a ranar yau Alhamis.
Wadannan shawarwari na gaba na da manufar tsagaita bude domin kawo karshen kazamin fadan da ake yi tsakanin bangarorin biyu da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a kasar Sudan ta Kudu, a cewar MDD. (Maman Ada)