Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya bayyana aniyarsa ta tattaunawa da tsohon mataimakinsa Riek Machar, da nufin shawo kan takaddamar siyasa dake neman jefa kasar ga yakin basasa.
Manzon musamman na kasar Amurka a Sudan ta Kudun Donald Booth ne ya bayyana hakan, jim kadan da kammala ganawarsa da shugaba Kiir a ranar Litinin.
Booth ya kara da cewa, shugaban Sudan ta Kudun ya amince ya gana da Machar ba tare da gindaya wani sharadi ba, muddin dai tsohon mataimakin nasa ya amince da gayyatar.
Har wa yau Booth ya bayyana cewa, tuni ya gana da wasu jiga-jigan jam'iyyar PLM mai mulkin kasar su 11, da a baya gwamnatin shugaba Kiir ta tsare, bisa zarginsu da hannu cikin abin da ta kira shirya juyin mulkin sojin ranar 15 ga watan nan da bai yi nasara ba. Wadannan jami'an jam'iyya, a cewar Mr. Booth, sun nuna sha'awar bada gudummawa ga yunkurin da ake yi na warware rikicin siyasar kasar cikin lumana.
Rahotanni daga kasar Sudan ta Kudu dai na nuna cewa, rikicin da ke yaduwa a sassan kasar na da alaka da rashin jituwa tsakanin dakarun sojin kasar masu biyayya ga shugaba Kiir, da kuma masu goyon bayan korarren mataimakinsa Riek Machar. (Saminu)