Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya bayyana a ranar Litinin cewa, zai bukaci kwamitin sulhu na MDD da ya kara karfafa ayyukansa na rukunin tawagar wanzar da zaman lafiya dake Sudan ta Kudu domin kawo karshen zafafar tashe-tashen hankalin kabilu. "Na dauki damarar ganin tawagar MINUSS ta tanadi kayayyakin aikin dake bukatu domin gudanar da muhimmin aikinta da ya shafi kare fararen hula." in ji mista Ban a yayin wani taron manema labarai da aka shirya a birnin New York sa'o'i kadan bayan dawowarsa daga kasar Philippines, inda ya je domin kimanta halin da ake ciki a wannan kasa tun bayan guguwar ruwan Haiyan.
"Za mu mai da hankali a wannan yini domin tattaunawa tare da shugabannin shiyyoyi da matakan karfafa aikin sojojin MDD na MINUSS, har ma da ba da taimako bisa kokarin siyasa don kawo karshen wannan rikici." in ji mista Ban tare da bayyana cewa, tawagar MINUSS tana kunshe yawan sojoji 6.800.
Rikicin na cigaba da karuwa a yankunan kasar tun cikin makon da ya gabata, bayan wani yunkurin juyin mulki da ake zargin sojojin dake biyayya ga tsohon maitaimakin shugaban kasar Riek Machar, 'dan kabilar Lour Nuer da aka sauke daga kujerarsa a cikin watan Yuli da kokarin hambarar da gwamnatin shugaba Salva Kiir, 'dan kabilar Dinka.
A ranar Alhamis din da ta gabata, wani harin da aka kai kan sansanin tawagar MINUSS a Akobo dake jihar Jonglei mai cikin tashin hankali, inda kimanin mayaka 2000 dauke da makamai suka kashe fararen hula 20 'yan kabilar Dinka da kuma sojojin MDD biyu, ana zargin 'yan kabilar Lour Nuer ne suka kai wannan hari.
Ban Ki-moon ya nuna babbar damuwarsa kan yawaitar kashe-kashen kabilu a cikin wannan rikici, lamarin da ya tilasta wa dubun dubatar mutane kaura daga wurarensu, musamman matune kusan dubu 45 suka samu mafaka a sansanonin MDD dake kasar domin samun kariya. (Maman Ada)