in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ware kudin Sin RMB biliyan 763 da miliyan 100 domin raya aikin gona
2012-04-27 17:25:19 cri

Ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Sin ta fayyace a ran 27 ga wata cewa, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar Sin ta ware kudin Sin RMB biliyan 763 da miliyan 100 domin raya aikin gona, wanda ya dauki kashi sama da 60 cikin dari na duk yawan kasafin kudin gwamnatin kasar Sin a fannin raya aikin gona.

A shekarar bana, gwamnatin kasar Sin ta ware kudin Sin RMB biliyan 1200 a farkon wannan shekara domin raya aikin gona, wanda ya karu da kashi 18 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, za a yi amfani da wadannan kudade wajen noma shuke-shuke da bincike kan kimiyya a fannin aikin gona da kuma raya fasahar aikin gona. Kana za a yi amfani da sauran kudin ga yin rigakafin bala'u da raya aikin ban ruwa a kananan gonaki da kula da kanana da matsakaitan koguna da kuma kaucewa bala'in ambaliyar ruwa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China