in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matsakaicin yawan karuwar kudin da Sin ta kebe wajen aikin gona ya kai kashi 21 cikin 100 a kowace shekara cikin shekaru 10 da suka gabata
2012-10-30 17:04:16 cri
Kwanan baya, bisa labarin da wakilinmu ya samu daga ma'aikatar kudi ta kasar Sin, an ce, daga shekara ta 2003 zuwa shekara ta 2012, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta kara kebe kudaden da yawansu ya zarce kudin Sin biliyan dubu 6 wajen aikin gona, wanda ke nuna karuwar adadin ya kai kashi 21 cikin 100 a ko wace shekara.

Aikin gona a kasar Sin ya shafi fannonin da suka hada da harkokin kauyuka, da manoma da abubuwan da suka shafi noma, kuma wannan ne ma ya sanya kasar kasancewa matsayin wata babbar kasa wajen aikin gona, abubuwan da suka shafi aikin gona na da muhimmanci kwarai da gaske, tun daga babban taron wakilai karo na 16 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a shekarar 2002, Sin ta mayar da aikin gona gaban kome. Da farko, gwamnatin tsakiya ta kara kebe kudin taimako wajen aikin gona, ya zuwa shekara ta 2012, yawan kudin taimakon da aka samu ya zarce kudin Sin Yuan biliyan 200, sa'an nan kuma gwamnatin tsakiya ta kara saka kudade wajen wannan sha'ani, baya ga kara kyautata manufofin da ke tallafawa wannan fanni, ya zuwa shekarar 2012 kuma yawan kudin da aka ware ya kai kusan Yuan biliyan 400 musamman domin manya gine-gine na kauyuka, ban da wannan kuma an kara kebe kudade wajen raya zamantakewar al'umma dake kauyuka.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China