in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin da Sin ta zuba ga manyan ayyuka uku na sha'anin noma zai kai fiye da biliyan 1000
2011-12-26 15:59:46 cri

Ranar Lahadi 25 ga wata, ministan kudi na kasar Sin Xie Xuren ya ce, sakamakon yadda Sin ta kara karfin taimakawa sha'anin noma, ana hasashe cewa, yawan kudin da za ta zuba ga manyan abubuwa uku da suka shafi sha'anin noma wato manoma, kauyuka da aikin gona zai kai kudin Sin RMB biliyan 1040 wanda ya karu da kashi 21 bisa 100 a wannan shekara.

A gun taron harkokin kudi da aka yi a wannan rana, Xie Xuren ya bayyana cewa, hukumar kudi ta kara daukar manufar nuna alfarma ga manoma da suke shuka hatsi, kuma ta daga farashin alkama da shinkafa taki kan taki da za ta kokarin taimakawa manoma wajen kara samun kudin shiga ta hanyar daukar matakai daban-daban. Ban da wannan kuma, Sin ta kara mai da hankali wajen ba da taimako ga masu fama da talauci tare da kafa wani tsarin kudi na kawar da fatara a dukkan fannoni. An yi hasashe cewa, cikin shekarar 2011, kudin da Sin za ta kashe a wannan fanni zai kai fiye da biliyan 220.

Xie Xuren ya bayyana cewa, a cikin shekara mai zuwa, hukumar kudi ta kasar Sin za ta kara bullo da manufofi na alfarma ga manoma tare da kyautata aikin noma yadda ya kamata.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China