in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Aljeriya ta samu rarar kudi a fannin kasuwanci na dalar Amurka biliyan 16.6 a karshen watan Satumba 2011
2011-10-24 16:08:56 cri

Ma'aunin daidaita sha'anin kasuwanci na kasar Aljeriya ya nuna cewa kasar ta samu rara kudi a fannin kasuwanci na dalar Amurka biliyan 16.67 a farkon tsawon watanni tara na shekarar 2011 bisa na dalar Amurka biliyan 13.84 a makamancin lokacin shekarar 2010 a cewar ma'aikatar kwastan ta kasar a ranar Lahadi.

Kayayyakin da ake fitar da su zuwa kasashen waje sun tashi ga dalar Amurka biliyan 51,73 bisa na makamancin lokacin shekarar data wuce dake dalar Amurka biliyan 43,70 wanda ya karu da kashi 18,36 cikin 100 a cewar wasu alkaluman wucin gadi da hukumar kididdiga ta kwastan CNIS ta kasar ta gabatar.

Kayayyakin da kasar take shigo da su an kiyasta su a dalar Amurka biliyan 35,05 bisa na makamancin lokacin shekarar 2010 dake dalar Amurka biliyan 29,86 inda aka samu karin kashi 17,40 cikin 100 a cewar hukumar CNIS.

Bunkasuwar kasuwancin waje nada nasaba da karin da aka samu na fiye da kashi 17 cikin 100 na fitar da man fetur zuwa kasashen waje, da kuma taimakon daidaituwar farashin gurbataccen mai a duniya a tsawon wannan lokacin a cewar hukumar.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China