in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU da FAO za su shirya wani taron koli domin yaki da yunwa a Afrika
2013-06-26 10:20:38 cri

Wani babban taro domin kawo karshen yunwa a Afrika zai gudana a ranar Lahadi a cibiyar kungiyar AU dake Addis Abeba, babban birnin kasar Habasha.

Wannan taron da za'a shirya cikin hadin gwiwa tsakanin kwamitin kungiyar tarayyar Afrika da kungiyar MDD kan abinci da noma (FAO), zai taimaka, a cewar wasu alkaluma, ga bullo da muhimman hanyoyi, siyasa da dabaru da aka tsara domin magance matsalar yunwa, dake ta'azarar da nahiyar Afrika, zuwa gabanin shekarar 2025, a cewar wata sanarwar kwamitin tattalin arzikin na MDD game da Afrika, wadda kuma shugaban kwamitin Carlos Lopes zai yi bayani a yayin wannan taro.

Hanyoyi da dabaru da za'a tsara za su yi dogaro kan samar da kayayyakin abinci ga tsarin kasa da na shiyya na Afrika kan noma (CAADP), da kuma wasu tsare-tsaren zuba jari kan noma da tsaron cimaka.

Haka kuma wannan taro zai mai da hankali kan matakan tallafawa kasashen Afrika, gwamnatocinsu da kungiyoyin zaman kansu wajen amfani da kwarewarsu domin taimakawa wasu kasashe ko yankuna.

Hakazalika, za'a fitar da wata sanarwa bayan wannan taro a ranar daya ga watan Yuli, dake bayyana niyyar siyasa ta mahalarta taron wajen bunkasa da hada kokarin mutanen Afrika da na kasa da kasa wajen yaki da yunwa, har da fasahohin zamani, karfafa jurewar yankunan karkara, sake gina yankunan karkara, da aiki tukuru wajen tsaron cimakan al'ummomin dake cikin birane. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China