Hukumar samar da abinci ta MDD ta bayyana a ranar Laraba cewa, kasashe 38 sun cimma mizanin kasa da kasa a kokarin yaki da yunwa, bitar nasarorin da ake son cimmawa gabanin wa'adin da aka tsara na shekarar 2015.
Babban darektan hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) Jose Graziano da Silva, ya ce, an tabbatar da kudurin wadannan kasashe a siyasance da hadin gwiwa na iya kawar da yunwa cikin hanzari,
Mataimakin kakakin MDD Eduardo del Buey ya shaida wa manema labarai cewa, kasashe 20 wadanda suka hada da Algeria, Bangladesh, Kamaru, Indonesia, Jordan, Nigeria, Togo, Uruguay, da sauransu sun cimma manufofin muradun karni na MDD na farko, wato kokarin rage wani adadi na masu fama da yunwa a kasashen nasu.
A cewar del Buey, babban jami'in na FAO ya bukaci dukkan kasashe da su kara himma da nufin kawar da yunwa kwata-kwata a duniya, kamar yadda babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya kaddamar a shekarar 2012.
Mr. del Buey ya ruwaito jami'in na FAO yana cewa, an samu nasarar rage matsalar yunwa a duniya baki daya a 'yan shekarun baya, amma har yanzu, akwai mutane miliyan 870 da ke fama da matsalar abinci mai gina jiki. (Ibrahim)