Kungiyar abinci da noma ta duniya (FAO) ta fitar da wani rahoto kwanan baya, inda ta bayyana cewa, kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara sun yi asarar fiye da dalar Amurka biliyan 4 ko wace shekara, dalilin rashin samun riba bayan aikin girbe albarkatun noma. Mista George Okech, wakilin kungiyar a kasar Zambia, ya bayyana cewa, ya zama wajibi kasashen dake wannan shiyya su gabatar da matakai da suka shafi rage wannan asara.
A cikin jawabinsa yayin wani taron kwararru kan rage asarar da ake samu bayan kammala aikin gona a kasashen Afrika dake kudu da hamadar Sahara a Lusaka, babban birnin Zambia, jami'in ya nuna cewa, wajibi ne kasashen shiyyar su fara tabo zancen daina batar da abinci.
A lokaci guda kuma, kungiyar AU ta bayyana cewa, rage asara bayan kammala aikin gona na da muhimmanci wajen bunkasa tsaron abinci, rage talauci, kafa hanyoyin samun riba da kuma bunkasa cigaban tattalin arziki a kasashen Afrika. (Maman Ada)