in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farashin abinci a duniya ya daidaita a Nuwamba
2013-12-06 10:31:35 cri

Rahotanni na nuna cewa, farashin kayayyakin abinci a duniya ya samu daidaito a watan Nuwamba, inda yadda farashin sukari ya kara sauka ya ingiza alkalumma kasa, duk da cewa, farashin man girki ya 'dan tashi, in ji hukumar kula da abinci da aikin noma ta MDD FAO.

Ofishin na FAO ya kuma kiyasta cewa, farashin hatsi a duniya da suka hada da shinkafa ya tashi zuwa wani sabon matsayi, lokaci daya a wannan shekarar, abin da shi ma yake nuna daidaiton farashin a bangaren kayan abinci.

Farashin ya tashi a watan Oktoban da ya gabata bayan da ya fadi a watanni biyar kafin haka ya dade a kan wannan farashi, idan aka duba na watan Oktoba, a Nuwamba yana nan a kan kashi 4.4 cikin 100 kasa da na bara.

Sai dai duk da zaman daidaito da farashin yake a 'yan watannin nan da kuma yadda ake cewa, zai cigaba a watanni masu zuwa, amma hukuma ta FAO a cikin rahoton shi na makomar hatsi da kayayyakin abinci ta yi hasashen samun bushewar yanayi saboda karancin ruwa a wassu kasashen dake yammacin Afrika kamar su Chadi, Mali, Mauritaniya, Niger da kuma Senegal, abin da zai kawo cikas wajen samar da abinci ya kuma kawo fargaban samun fari da zai kai a shekara mai zuwa.

Ya zuwa yanzu dai wannan shekarar ta 2013, ya kasance cikin daidaito a shekaru 5 da suka gabata, sakamakon wani yanayi da ba'a saba gani ba na farashin abinci a shekara ta 2012.

Bayanin hukumar FAO game da yanayin abinci na duniya zai fito a ranar 9 ga watan Janairu da ke tafe. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China