Babban sakatare na MDD Ban Ki-moon ya yi kira a ranar Litinin ga shugabannin kasashen duniya da su yi koyi da Nelson Mandela domin taimakawa zaman lafiya a cikin sabuwar shekara mai zuwa. A yayin taron menama labarai na karshen wannan shekara, da ya ba da a cibiyar MDD dake birnin New York, mista Ban ya bayyana cewa, shekarar 2013 za ta tsaya a matsayin shekarar da duniya ta yi babban rashi da yi wa Mandela gani na karshe. "Ban yi tunanin komi yanzu da zai faranta raina a shekarar 2014 ba, sai dai ina son ganin shugabannin duniya baki daya su dauki misali kan Mandela domin cika alkawuran da suka dauka na siyasa da na zaman rayuwa." in ji mista Ban.
Nelson Mandela ya zama shugaban farko bayan mulkin wariyar launin fata da aka zabe shi ta hanyar siyasa a kasar Afrika ta Kudu bisa babban sakonsa na sasantawa da hada dukkan 'yan kasar Afrika ta Kudu wuri guda.
Allah ya yi masa rasuwa a ranar 5 ga watan Disamban a lokacin da yake da shekaru 95 a duniya bayan ya kwashe watanni da dama yana fama da ciwo.
An sauko da tutocin MDD kasa a ranar Jumma'ar da ta gabata a cibiyar MDD dake birnin New York domin girmama ranar bukukuwan jana'izar Mandela.
Babban taron MDD zai shirya wani biki a ranar Alhamis domin martaba Mandela, mutumin da ya zama misalin aikin da muke yi ko wace rana, in ji mista Ban Ki-moon. (Maman Ada)