in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta cika alkawarinta na tabbatar da tsaro a yankin tekun Pasha, in ji ministan tsaron kasar
2013-12-08 16:59:02 cri
A jiya Asabar 7 ga wata, an ci gaba da taron Manama yadda ya kamata, inda ministan tsaron kasar Amurka, Chuck Hagel ya bayyana cewa, Amurka za ta ci gaba da kokarin cika alkawarinta na tabbatar da tsaro a yankin tekun Pasha.

Taken jawabin da mista Hagel ya yi a gun taron Manama a jiya shi ne batutuwan tsaron duniya dake gaban komai ga Amurka, inda aka tabo maganar batun nukiliya na Iran, da kuma yadda za a kara hadin gwiwa da kasashen dake yankin tekun Pasha a fannin tsaro. Mista Hagel ya furta cewa, Amurka za ta ci gaba da kokari a fannin siyasa da kuma aikin soja, da zummar cika alkawarinta na tabbatar da tsaro a wannan yanki. Ban da haka, Mista Hagel ya kara da cewa, Yanzu Amurka ta jibge sojojin kasa da na sama da na teku kimanin dubu 35 a yankin tekun Pasha, tare da manyan kayayyakin aikin soja da dama, kamarsu tankuna, jiragen saman yaki da sauransu. Amurka za ta ci gaba da kokarinta, ta yadda za ta ba da kariya ga aminanta a yankin Gabas ta Tsakiya da na tekun Pasha.

Ranar 24 ga watan Nuwamban bana, an cimma matsaya kan mataki na farko na daidaita batun nukiliya na Iran tsakanin kasashe shida da kasar Iran, wato Iran ta daina tace sinadarin Uranium yayin da kasashen yammacin duniya su kuma zasu soke wasu matakan takunkumi da aka kakaba wa Iran. Wannan yarjejeniya ta janyo fargaba ga wasu kasashe dake yankin tekun Pasha, kamar Saudiya da sauransu. Game da wannan batu, a cikin jawabinsa a jiya, mista Hagel ya jaddada cewa, Amurka ba za ta rage yawan sojoji da ta jibge a yankin tekun Pasha ba a sakamakon daddale yarjejeniya da Iran, da kuma raguwar yawan kasafin kudin gwamnatin kasar Amurka ta fuskar soja.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China