in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya lashi takwabin warware kalubalen da ake fuskanta a yankin Sahel
2013-12-13 10:34:52 cri

Kwamitin sulhu na MDD, ya jaddada kudurinsa na magance matsalar tsaro da na siyasa da ake fuskanta a kasashen Afirka da ke yankin Sahel.

Babban sakataren MDD Ban Ki-moon ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis, yayin da yake yiwa kwamitin jawabi game da rangadin da ya kai kasashe 4 da ke yankin tare da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim a makon da ya gabata, wadanda suka hada da Mali, Nijar, Burkina-Faso da Chadi.

Yayin ganawar, kwamitin ya amince da sanarwar shugaba game da yankin na Sahel, inda aka kara nuna damuwa tare da yin allah-wadai da yadda 'yan ta'adda da sauran kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi ke take hakkin bil-adama, cin zarafin faren hula, musamman mata da kananan yara a yankin.

Mr. Ban ya yi gargadin cewa, ayyukan ta'addanci, fataucin makamai, miyagun kwayoyi da kuma mutane da sauran miyagun aikace-aikace, barazana ce ga harkokin tsaro na shiyyar. Don haka, ya yi kiran da a kara daukar matakan da suka dace don magance matsalar abinci da ta addabi yankin.

A nasa bangare, kwamitin mai mambobi 15, ya nanata yin kira ga kasashen da ke yammacin Afirka da yankin Maghreb, da su karfafa yin hadin gwiwa tare da bullo da matakai masu inganci da za su taimaka wajen kawar da ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda, hana yaduwar makamai, yaki da miyagun laifuffuka, ciki har da ayyukan da suka shafi fataucin miyagun kwayoyi a yankin na Sahel. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China