Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon da shugaban gungun bankin duniya Jim Yong Kim sun bayyana niyyarsu a ranar Laraba game da tallafawa tsarin da ya shafi kyautata lafiyar mata da kuma ilmintar da yara mace a yankin Sahel na Afrika da kuma zuba dalar Amurka miliyan 200 kan wani sabon tsarin shiyya da zai taimakawa wadannan maradu.
Mista Ban ya sanar da kaddamar shirin baiwa cin gashin kansu a yankin Sahel dake kunshe da dalar Amurka miliyan 200 a birnin Niamey na kasar Nijar a yayin wani rangadin tahiri na manyan jami'ai biyar na kungiyoyin kasa da kasa a wannan shiyya wato MDD, bankin duniya, AU, bankin raya Afirka da kuma EU. Wannan shiri ya biyo bayan kira game da kasar Nijar dake shafar manufar kyautata kiwon lafiyar mata da ilmin yara mace, in ji mista Farhan Haq, mataimakin kakakin MDD a yayin wani taron manema labarai. A cewarsa, bankin duniya zai kara zuba dalar Amurka miliyan 150 a tsawon shekaru biyu masu zuwa domin taimakawa tsare-tsaren kiwon lafiyar mata da yara kanana a cikin wannan shiyya. (Maman Ada)