Babban magatakardar MDD Ban ki-Moon, ya yi kira da a dauki karin matakan magance matsalolin dake addabar yankin Sahel cikin dogon lokaci.
Ban, wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, yayin babban zaman MDD da aka gudanar don gane da yankin, ya bayyana manyan matsalolin dake addabar yankin na Sahel, da suka hada da karancin tsaro, da matsalar isasshen abinci, da barkewar annoba da kuma halin matsi da al'ummunsa ke ciki.
Duk da tarin matsalolin dake addabar wannan yanki na nahiyar Afirka, a hannu guda, Mr. Ban ya ce, ana samun ci gaba sannu a hankali a cikin 'yan shekarun nan, don haka ya jaddada bukatar kara kaimi wajen magance kalubalen da ake fuskanta, ta hanyar samar da kwakkwaran shirin jin kai da za a sanya gaba cikin dogon lokaci.
Bugu da kari, Ban ya ce, ya amince da shirin samar da ci gaba, da wakilin majalisar dinkin duniya na musamman a yankin na Sahel, Romano Prodi ya gabatar a farkon wannan shekara, yana mai cewa, shirin ya tanaji shigar da dukkanin masu ruwa da tsaki a ci gaban yankin, cikin shirin warware matsalolin da ake fuskanta cikin dogon lokaci.
Wannan yanki dai na Sahel ya kunshi kasashen Burkina Faso, da Kamaru, da Chadi, da Mali, da Mauritania, da Niger, Senegal, Gambia, da kuma Nigeria. (Saminu)