A ranar Talata aka bude taron baje koli karo na farko kan karfafa dabarun magance matsalar karancin abinci a yankin Sahel da yammaci da gabashin Afrika a birnin Ouagadougou na kasar Burkina-Faso a karkashin jagorancin faraministan kasar, Luc Adolphe Tiao.
Ana gudanar da taron cikin hadin gwiwa tsakanin kwamitin din din din na kasashen dake yaki da fari a yankin Sahel na CILSS da kungiyar FAO, kuma bikin baje kolin na tsawon kwanaki uku ya hada kwararru fiye da 200 da suka fito daga kasashen Afrika da dama. An bayyana cewa, babban makasudin shirya wannan haduwa shi ne don karfafa kwarewar hukumomi da kungiyoyi da abin ya shafa wajen dauka da aiwatar da matakan da suka wajaba domin kara kyautata karfin mutanen yankin Sahel da na yammacin Afrika wajen fuskantar matsalolin karancin abinci da makamantansu.
Haka zalika bikin baje kolin ya kasance wata dama ta yin musanya tsakanin mahalarta taron, ta yadda za'a iyar bullo da hanyoyi da dabarun da suka wajaba da za su amfana wa wadannan shiyyoyin yammancin Afrika biyu. (Maman Ada)