A ranar ta 6 ga wata ne, wasu shugabannin kasashen Afirka sun mika ta'aziyya bisa ga rasuwar tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Mandela.
Tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana a ranar 6 ga wata cewa, rasuwar Mandela ta sa kasar Afirka ta Kudu ta rasa wani jagori, kuma nahiyar Afirka ta rasa wani mutum mai daraja, kuma duniya ma ta rasa wani muhimmin shugaba. (Zainab)