Shugaba Jacob Zuma ne ya sanar da hakan, bayan ya gana da iyalan marigayin a jiya Jumma'a. Zuma ya kara da cewa, za a binne marigayi Mandela a garinsa na haihuwa, wato Qunu dake lardin Eastern Cape da ke kudancin kasar, bayan zaman makoki na kwanaki 10 da za a yi kafin binne gawar tasa.
Bisa tsarin bikin binne mamacin, an sanya ranar 8 ga wata ta zama ranar addu'o'i da jimamin rasuwar tsohon shugaban, sai kuma ranar 10 ga wata, wadda za ta zama ranar addu'o'i na musamman a hukunce, wadanda za a yi a birnin Johannesburg. Ana kuma sa rana ajiye gawar tasa a wani babban ginin ofishin hukumar kasar dake birnin Pretoria, tsakanin ranekun 11 zuwa 13 ga wata.(Saminu)