Li Yuanchao ya nuna alhini a gaban mutum-mutumin na Mandela, inda ya rubuta sakon ta'aziyya a littafin da aka kebe don mika sakon ta'aziyya. Kana Li Yuanchao ya bayyana cewa, Mandela ya yi kokarin kiran samun daidaici da sulhuntawa a tsakanin kabilu daban daban na kasar. Ya kasance jarumi a cikin zuciyar jama'ar kasar Afirka ta Kudu, kana kasa da kasa sun nuna yabo gare shi. A madadin gwamnatin kasar Sin da jama'arta, Li Yuanchao ya mika ta'aziyya bisa ga rasuwar Mandela. (Zainab)