A ran 6 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sako ga takwaransa na kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma,inda ya mika ta'aziyyarsa bisa ga rasuwar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.
A madadin gwamnatin kasar Sin da shi kansa, Mista Xi yana nuna juyayi matuka bisa ga rasuwar Mandela, tare da mika ta'aziyya ga 'yan uwansa.(Danladi)