Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya mika ta'aziyya matuka bisa ga rasuwar Mandela a lokacin da yake zantawa da takwaransa na kasar Faransa Jean-Marc Ayrault a safiyar ranar alhamis 6 ga wata.
Mista Li ya ce, an wayi gari da labarin rasuwar Mista Mandela mutumin da daukacin kasashen duniya suke girmamawa, hakan ya sa jama'a cikin wani hali na juyayi da bakin ciki sosai, gwamnatin kasar Sin da jama'arta na mika ta'aziyya matuka ga gwamnatin kasar Afirka ta Kudu, da jama'arta, da kuma 'yan uwan Mr. Nelson Mandela (Danladi)