Bugu da kari a wasikar, shugaba Jonathan ya bayyana bakin cikinsa dangane da rasuwar Madiba, inda ya kara bayyana shi a matsayin mutum mai hangen nesa, karfin hali da sanin ya kamata, kana jagoran shimfida mulkin demokiradiya na gaskiya.
Ya kuma yi amfani da wannan dama wajen mika alhinin 'yan Najeriya ga shugaba Zuma da daukacin al'ummar kasar Afirka ta Kudu, yayin da suke makokin marigayi Mandela, gwarzon yaki da nuna wariyar launin fata.(Ibrahim)