in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika ta'aziyyar ta bisa ga rasuwar Mandela
2013-12-06 10:01:27 cri

A ran 6 ga wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei ya mika ta'aziyyar kasar bisa ga rasuwar tsohon shugaban kasar Afrika ta kudu Nelson Mandela. Yana mai bayyana shi da wani tsohon abokin al'ummar kasar Sin.

Hong Lei ya ce, Mista Mandela wani shahararren shugaba ne da yayi yaki da wariyar launin fata wanda kuma ya kafa sabuwar kasar Afirka ta Kudu, sannan wani dan siyasa ne da ya shahara a duniya. A don haka ba kawai jama'ar kasar Afirka ta Kudu ke girmama shi a matsayin 'mahaifin kasa' ba, hatta al'ummar kasashen duniya suna girmama shi da kuma kaunar sa.

Mr. Hong ya kara da cewa, Mista Mandela tsohon abokin jama'ar kasar Sin ne, wanda ya bayar da gudummawa mai ma'ana a tarihi wajen kafa dangantakar Sin da Afirka ta Kudu tare da raya ta.

A don haka Mr. Hong ya ce, Kasar Sin na nuna matukar juyayinta da mika ta'aziyya bisa ga rasuwar Mandela ga gwamnatin kasar Afirka ta Kudu, da jama'arta, da kuma 'yan uwan Mr. Nelson Mandela.(Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China