in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jihohi biyar dake fama da bala'in ambaliyar ruwa na Sin, sun samu kudin agaji
2013-08-24 17:15:06 cri

A ranar Jumma'a 23 ga wata, ma'aikatar kudi da ta harkokin jama'ar kasar Sin sun bai wa jihohin da bala'in ambaliyar ruwa ya aukawa agaji kudi da yawansu ya kai yuan miliyan 580. Jahohin da suka samu wannan agaji sun hada da Liaoning, da Jilin, da Heilongjiang, da Guangdong, da kuma jihar Guangxi.

Bayanai sun nuna cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen tsugunar da mutanen da suka rasa gidajensu sakamakon wannan bala'in, da ciyar da su, da gyara masu gidajensu da suka lalace, da kuma jajantawa iyalan wadanda suka mutu a sakamakon abkuwar lamarin, duka dai a kokarin tabbatar da jin dadin rayuwar jama'a yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China