Gwamnatin Najeriya ta amince da gina wata sabuwar tashar jiragen ruwan teku mafi zurfi, a dukkanin fadin nahiyar Afirka kan kudin da yawansu ya kai naira miliyan dubu 216.
Ana sa ran kammalar sabuwar tashar ta Lekki ne dai nan da shekaru hudu masu zuwa, ana kuma fatan bude ta zai warware matsalar cinkoson kayayyakin da ake fama da ita a tashoshin ruwan kasar daban daban.
Da yake tabbatar da hakan jim kadan da kammala taron majalissar zartaswar kasar a ranar Laraba 4 ga watan nan, ministan yada labarun kasar Labaran Maku, ya ce, sabuwar tashar da ake fatan ginawa, mai fadin hekta 90, za ta iya karbar tan miliyan hudu na kayan fito a lokaci guda. Maku ya kara da cewa, tashar ta Lekki za ta samarwa kasar tarin kudaden shiga da zarar an kamamla ta.
Shi ma a nasa tsokaci kan wannan batu, ministan ma'aikatar sifirin kasar Idris Umar, cewa ya yi, baya ga rage cinkoson kayayyaki a tashoshin ruwan kasar, sabuwar tashar za ta kuma samarwa al'ummar kasar guraben ayyukan yi sama da 162,000. (Saminu)