in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nigeriya yana neman masu zuba jari a wani taro a Landan na Ingila
2013-11-20 12:11:13 cri

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeriya a Laraban 20 ga wata ya tashi zuwa birnin Landan na kasar Ingila domin shugabantar wani taro na kwanaki uku da kungiyar manyan masu zuba jari ta duniya ta kira.

Kamar yadda sanarwar fadar shugaban ta fitar, an ce, abin da za'a tattauna a wajen taron sun hada da tsawon lokacin da za'a dauka ana samar da kudaden aiwatar da ayyuka a Nigeriyan, in ji Rueben Abati, mai ba da shawara kan harkokin watsa labarai da farfaganda na shugaban kasar a Abuja, babban birnin kasar Nigeriya.

Abati ya nuna cewar, wannan taron da uwargida Lynda Chalker ta shirya ba kawai zai tattauna kundin tsarin yada labarai da sadarwa na kasar Nigeriya ba ne, har ma tsarin cigaba da kasar ke da shi ga masu zuba jari, ta yadda zai ja hankalin masu zuba jari da sauran 'yan kasuwa.

A cikin bayanin da Abati ya fitar, an ce, a wajen taron, kungiyar hadin gwiwwa da cigaban tattalin arziki, za ta yi nazari kan tsarin da kasar ke da shi a yanzu haka, kuma ministoci da shugabannin hukumomin da suka rufa wa shugaban kasar baya za su yi bayani ga taron game da cigaban da ake samu a ma'aikatunsu, sannan su jagoranci wassu tattaunawa a kan wadansu shirye-shiryen da ake son bullowa da su domin dakile irin kalubalolin da za'a fuskanta.

A lokacin wannan ziyayar, shugaba Jonathan ya samu rakiyar wassu zababbun gwamnoni da ministoci, har ma da shugabannin hukumomin na kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China