in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya ta samu naira biliyan 9 sakamakon shirin kanana da matsakaitan kasuwanci
2013-11-18 12:04:38 cri

Gwamnatin tarayyar Nigeria tare da hadin gwiwwar bankin masana'antun kasar a shirinta da ta aiwatar wa kanana da matsakaitan kasuwanci a jihohi 17 wato NEDEP ta samu ribar kudin kasar naira biliyan 9 a wani yunkuri na farfado da ayyukan dogaro da kai.

Ministan masana'antu, kasuwanci da zuba jari Mr. Olusegun Aganga ya bayyana hakan lokacin da yake kaddamar da shirin na NEDEP a garin Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa dake kudancin Nigeriya a ranar Jumma'ar da ta gabata.

Mr. Aganga ya lura cewa, kaddamar da shirin wani yunkuri ne na gwamnatin tarayyar na ganin ta sake daidaita matsayin da kuma cigaban kanana da matsakaitan kasuwanci a wani babban mataki na habaka tattalin arziki ta hanyar hadin gwiwwa da jihohi wajen samar da ayyukan yi da kuma arzikin kasa.

Ministan ya jaddada cewa, wannan shirin na NEDEP, an shirya shi ne musamman domin shawo kan manyan kalubalolin da ke hana cigaban kanana da matsakaitan kasuwanni a fadin kasar, yana mai bayanin cewa, gwamnatin tarayya tana hadin gwiwwa ne da sauran jihohi na kasar domin ganin an samar da ayyukan yi, an kuma rage adadin marasa aikin yi. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China