Karamin ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya Dr. Nurudeen Mohammed, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki na kungiyar ECOWAS, da su tabbatar da daukar dukkanin wasu matakai, da za su haifar da yanayin zaman lafiya da tsaro a yankunan dake yammacin Afirka.
Nurudeen wanda darakta mai lura da al'amuran kungiyar ta ECOWAS a ma'aikatar harkokin wajen Najeriyar Ali Ocheni ya wakilta, ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, cikin jawabin bude taron tuntuba karo na 4, don gane da zakulo hanyoyin aiwatar da kudurorin kungiyar ta ECOWAS da aka fara gudanarwa. Ministan ya bayyana tashe-tashen hankula dake addabar wannan yanki, a matsayin dalilan dake kawo koma baya, yana mai cewa, babu wani ci gaba na hakika da za a iya samu, muddin dai aka gaza wanzar da kyakkyawan yanayin tsaro da kwanciyar hankali.
Daga nan sai ya yi fatan taron na wannan karo, zai mai da hankali ga bankado sabbin hanyoyin sauya alkiblar kungiyar, zuwa ga dabarun wanzar da zaman lafiya, da tsaro, da samar da daidaito a yankin na yammacin Afirka.
Da take tofa albarkacin bakinta yayin zaman na wannan lokaci, babbar jami'ar kungiyar mai kula da harkokin siyasa Salamatu Suleiman, cewa ta yi, rigingimu da tashe-tashen hankula na ci gaba da haifar da kalubale ga wannan yanki tsahon kusan shekaru 20, don haka a cewarta, taron na wannan lokaci zai nazarci hanyoyin magance lamurran da suka shafi dalilan barkewar tashe-tashen hankula a yankin. (Saminu)