Wasu 'yan jarida sun aza ayar tambaya kan cewa, bayan da kasar Sin ta shata yankin tsaron sararin samaniya a yankin tekun Gabas na kasar, ma'aikatar harkokin wajen kasar Japan ta nuna adawa da wannan yankin na tsaron sararin samaniya da Sin ta shata wanda ke kunshe da tsibirin Diaoyu a ciki, tare da bayyana bukatar yin shawarwari tare da kasar Sin kan wannan batu, ko wane martani da Sin za ta bayar game da batun?
Qin Gang ya ce, gwamnatin Sin ta riga ta bayar da ka'idoji da kuma abubuwan da ta yi la'akari da su wajen shata yankin tsaro na sararin samaniya, kuma kasar Sin ta dauki wannan mataki yadda ya kamata kuma bisa tushen kundin tsarin mulki na M.D.D. da dokokin kasa da kasa.
Qin Gang ya sake nanata cewa, tsibirin Diaoyu da tsibiran da ke kusa da shi mallakar kasar Sin ne, kuma kasar Sin za ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da mulkin wadannan tsibirai. Kasar Sin ta bukaci Japan da ta daina daukar matakan da za su kawo baraka ga cikakken yankin kasar Sin, kuma ya kamata Japan ta yi kokari yin tattaunawa da kasar Sin domin warware takaddama dake tsakaninsu.(Bako)