A cikin asusun ba da tallafi ga aikin jarida, na wannan shekarar 2013, kafofin watsa labaru da suka hada da jaridu, rediyo da talabijin masu zaman kansu na kasar Nijar za su samu damar rarraba kudin Sefa miliyan dari biyu tsakaninsu da gwamnatin kasar Nijar ta kebe wa wadannan kafofi. Mataimakin shugaban babbar hukumar sadarwa ta CSC, Ali Ousseini ya gabatar da rabon wadannan kudade a ranar Jumma'a a birnin Niamey bisa tushen matakan da sharudan suka dace na samun wannan taimako, musamman ma ta yin la'akari da yanayin wadannan kafofi da kuma nauyin da ya rataya kansu.
A wannan shekara, kimanin jaridu ishirin, gidajen rediyo goma sha biyar da gidajen talebijin bakwai za su raba wannan ganima tsakaninsu, kuma mukasudin wannan taimako na gwamnatin kasar Nijar shi ne don taimaka wajen zamanintar da kayyayakin aiki na wadannan kafofi, da kyautata jin dadin ma'aikata domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata a bangaren kafofin watsa labarai masu zaman kansu a kasar Nijar. (Maman Ada)