Bikin nune-nunen kayan jiki na kasa da kasa da aka fi sani da FIMA karo na tara ya soma a ranar Laraba da yamma a zauren wasanni na "Palais du 29 Juillet" dake Niamey a karkashin jagorancin ministan al'adun kasar Nijar, Ousmane Abdou, tare da matar shugaban kasa madam Issoufou Malika a matsayin tauraruwar bukukuwan FIMA, haka kuma an samu halartar faraminista Brigi Rafini da manyan jami'an kasar Nijar da na kasashen waje.
Bikin FIMA wata muhimmiyar haduwa ce ta fitattun madunka, masu tsare-tsaren dunki, taurarun gwajin tufafi da sauran kwararru a fannin dunke-dunken zamani. Kimanin baki fiye da 1500 daga kasashe hamsin ne suke halartar wannan biki, kuma ana sa ran zuwan matan shugabannin kasashen Afrika biyar a wannan biki da aka fara ranar 20 har zuwa 25 ga watan Nuwamba.
A cikin wadannan kwanaki shida wato daga ranar 20 zuwa 25 ga wata, birnin Yamai yana cikin bushashar kide-kide da nune-nune tufafi.
Bikin FIMA na shekarar 2013 ya kasance bisa jigon aikin kirkirowa domin taimakawa zaman lafiya a Afrika.
A cewar shugaban bikin FIMA, Seidnaly Sidi Ahmed da aka fi sani da Alphadi, kasar Nijar kasa ce mai zaman lafiya, domin haka ya kamata masu zuba jari su kara mai da hankali kan kasar. Haka shi ma wani babban dandali ne na kasa da kasa da ke kara daga matsayin kasar Nijar a duniya. (Maman Ada)