Babban sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon zai kai wani rangadin aiki a ranar shida ga watan Nuwamba mai zuwa a kasar Nijar, a wani labarin da ya fito daga ofishin wakilcin majalisar dake birnin Yamai.
A yayin wannan ziyara da za ta kai shi kuma a kasar Mali, mista Ban zai samu rakiyar manyan jami'an bankin duniya, asusun IMF, bankin cigaban Afrika da shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Afrika, madam Nkosazana Dlamini-Zuma.
Wannan ziyara ta babban jami'in MDD zai mai da hankali kan batun tsaro a yankin Sahel, a cewar wata majiyar dake kusanci da wannan batu. (Maman Ada)