in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya kammala ziyarar aikinsa a kasar Nijar
2013-11-07 14:25:27 cri

Sakatare janar na MDD, mista Ban Ki-moon ya isa birnin Yamai a ranar Labara da safe a karkashin wata tawagar manyan jama'ai.

Shugaban MDD ya samu rakiyar shugabar kwamitin tarayyar Afrika madam Nkosazana Dlimini-Zuma, shugaban bankin duniya mista Jim Yong Kim, shugaban bankin cigaban Afrika (BAD) mista Donald Kaberuka da kuma wakilin kwamitin kungiyar tarayyar Turai, Andris Piebalgs. Tawagar ta hadin gwiwa ta samu tarbo a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Diori Hamani dake birnin Yamai daga faraministan Nijar malam Brigi Rafini mai kewaye da mambobin gwamnatin Nijar da jakadun kasashen waje da wakilan manyan hukumomin kasa da kasa dake Nijar.

A cewar ministan harkokin wajen kasar Nijar Bazoum Mohamed, wannan ziyara ta manyan jami'an duniya a cikin kasashen yankin Sahel, musamman a kasashen Mauritania, Mali, Nijar, Burkina-Faso da kasar Chadi ta rataya kan batutuwan da suka shafi mulki na gari, tsaro da bunkasa dabarun samun cigaba.

A tsawon ziyarar, mambobin tawagar ta tattauna tare da shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou, shugaban majalisar dokoki Hama Amadou, mambobin gwamnati da kuma wakilan fararen hula.

A cikin jawabinsa a gaban 'yan majalisar dokokin kasar Nijar mista Ban Ki-moon ya bayyana jin dadinsa kan kokarin da gwamnatin Nijar take yi na cimma muradun sabon karni na samun bunkasuwa, da kuma wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Sahel da ma duniya.

Hakazalika bangarorin biyu sun gudanar da taron manema labarai na hadin gwiwa na karshen wannan rangadi tsakanin Mahamadou Issoufou da Ban Ki-moon tare kuma da sanya hannu kan wasu manyan yarjejeyoyi guda hudu tsakanin gwamnatin Nijar da Tarayyar Turai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China