in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijar ta bankado wasu mutanen dake fataucin 'yan ci rani
2013-11-19 10:40:19 cri

Hukumomin kasar Nijar sun bankado wani gungun mutane kusan talatin dake fataucin 'yan ci rani, kuma an cafke wasu daga cikinsu, a wani labari da huhumomin kasar suka bayar a ranar Litinin.

A cewar ministan shari'ar kasar Nijar kuma kakakin gwamnati, malam Marou Amadou, a cikin mutanen da aka gurfanar, akwai 'yan sanda, direbobi da masu sayen motoci. Jami'an tsaron kasar ne suka gano wannan gungun mutane a Agadez da Arlit, muhimman biranen kasar da ke kasancewa manyan cibiyoyin ratsawa da 'yan cin ranin kasashen yammacin Afrika, in ji minista Marou Amadou.

Wannan aiki na jami'an tsaro ya biyo bayan mutuwar 'yan ci ranin kasar Nijar 92 sakamakon rashin ruwan sha a cikin watan Oktoban da ya gabata, wadannan mutane da ke hada da kananan yara 52, mata 33 da namiji 7, sun rasa rayuka bayan motarsu ta lalace a tsakiyar hamadar Sahara da ke kusa da kan iyaka da kasar Aljeriya. Wasu daga cikin mutanen dake da hannu kan wannan lamari, an cafke su ne a jihar Damagaram dake kudancin kasar, yankin asali ne na mutanen da suka mutu a kan hanyarsu ta tsallakawa zuwa wata kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China