A ranar Lahadi 24 ga wata ne shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir da takwaransa na Eritrea Isaias Afwerki, suka kaddamar da bikin baje kolin harkokin yawon shakatawa da sayayya karo na 7 a Port-Sudan, babban birnin jihar Bahar asawad da ke gabashin Sudan.
Shugaba al-Bashir ya ce, bikin baje kolin harkokin yawon shakatawan ya bayar da gudummawa wajen bunkasa harkokin tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a a jihar Bahar asawad tare da nuna albarkatun yawon shakatawa na Sudan.
A halin da ake ciki, al-Bashir ya yaba dangantakar da ke wanzuwa tsakanin sassan biyu, yana mai cewa, Sudan na mu'amala da kasar Eritrea tun lokacin da take karkashin mulkin mallaka, lamarin da ya taimaka wajen 'yantar da kasar ta Eritrea, kokari da a yau, ya ce, ya taimakawa wajen cimma muradun al'ummomin kasashen biyu.
Bayanai na nuna cewa, a kan shirya wannan biki ne a tsakiyar watannin Nuwamba da Fabrairun ko wace shekara, kuma shi ne bikin baje kolin harkokin yawon shakatawa mafi girma da ake shiryawa a Sudan, kuma ta wannan biki ne jama'a ke kara sanin kayayyakin al'adu na jihar Bahar asawad da ke gabashin Sudan. (Ibrahim)