in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta nuna damuwa sosai game da tashe-tashen hankali a Libya
2013-11-18 10:18:23 cri

Shugabar kwamitin tarayyar Afrika AU, Nkosazana Dlimini-Zuma ta nuna damuwarta da bacin rai game da tashe-tashen hankalin baya bayan nan a birnin Tripoli da suka janyo mutuwar mutane da dama, in ji gamayyar kasashen Afrika a cikin wata sanarwa.

Madam Zuma ta nuna kaduwarta matuka game da zafin rikici da rashin doka a kasar Libya a makonnin baya bayan nan, ji wannan sanarwa.

Jami'ar ta yi allawadai da amfani da karfin yaji a cikin kasar, musammam ma kan fararen hula dake zanga-zanga cikin lumana. Zuma ta yi kira ga bangarorin da abin ya shafa a kasar Libya da su yi kokarin warware sabanin dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari bisa tushen dokokin da kasar ta tanada tare da jaddada cewa, kungiyar AU za ta cigaba da tallafawa gwamnatin Libya domin maido da zaman lafiya a wannan kasa dake arewacin nahiyar Afrika.

Kasar Libya dai na fama da tashe-tashen hankali tun bayan faduwar gwamnatin Gaddafi shekaru biyu da suka gabata, har yanzu hukumomin Libya na nuna kasawa wajen daidaita matsalar kungiyoyin sa kai masu makamai a cikin wannan kasa.

A ranar Jumma'a ne wasu sojojin sa kai suka afkawa fararen hula masu zanga-zanga a birnin Tripoli da suke bukatar wadannan dakarun sa kai da su fice daga babban birnin, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 42 tare da jikkata 460, a cewar ma'aikatar cikin gidan kasar Libya. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China