Jami'ai sun baiyana ranar Talata cewa, dakarun gwamnatin kasar Somaliya sun lalata maboyar kungiyar Al-Shabaab guda 17, kana sun cafko 'yan kungiyar guda 40, a wani sumame da aka kai a Mogadishu, babban birnin kasar ta Somaliya.
Yayin da yake zantawa da 'yan jarida dangane da tabarbarewar harkokin tsaro a babban birnin kasar, ministan harkokin cikin gida da tsaron kasa Abdelkarim Hussein Guled ya baiyana cewa, wadanda ke wadannan maboya ne ke kawo rashin tsaro da tayar da hankulan 'yan kasar Somaliya.
Ya ci gaba da cewa, a kowace maboya, akwai mambobin kungiyar tsakanin 3 zuwa 11, wanda baki daya yawansu ya kai 39, kuma hukumomin tsaro na kasar suna nemansu ruwa a jallo.
Harkokin tsaro sun tabarbare a Mogadishu, babban birnin kasar a cikin 'yan makonnin nan, musamman a cikin watan Ramadan mai tsarki, wanda ya kare a makon da ya wuce. (Lami)